<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>149</hymn_number>
<title>Ya Ku Zukatan Mutane LW149</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya ku zukatan mutane,
 Rashin sani kuka yi,
 Kamar ƃatattun tumaki,
 Wurin kiwo ku ke ki.

[V2]
 2) Ko kun san wani kamarsa?
 Almasihu ya fi duk
 Ƙauna, taimako, har kuma
 Ceto daga zunubi.

[V3]
 3) Ya ku zukatan mutane,
 Shakka ce ta hana ku?
 Sai ku dogara gare shi
 Wanda ya ke ƙaunarmu.

[V4]
 4) Sai ku zo, ku ji, ku gwada,
 Yesu mai aminci ne.
 Maimakonmu shi ya cika
 Nufin Ubanmu daidai.

[V5]
 5) Cikin Yesu mu ke samun
 Sanin Allah, sanin rai.
 Kuma aka ɗora masa
 Duk alhakin zunubai.

[V6]
 6) Da kun gaskata maganar,
 Da ya sake halinku,
 Da ya sabonta zukata,
 Da ya zauna cikinku.

[V7]
 7) Ƴanuwa, mu yi godiya,
 Sai mu ƙaunace shi dai.
 Ba dalilin tsoro kuma
 Har iyakar zamanai.</lyrics>
</song>